Bayan dawowarshi daga kasar Jordan, anan sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai kai ziyarar aiki jihar Kano ranar laraba me zuwa, 6 ga watan Disamba, gwamnatin jihar Kano ta fara shirye-shiryen tarbar shugaban kasar, anan gwamnan jihar ne, Abdullahi Umar Ganduje, yakai ziyarar karshe, asibitotcin Giginyu dana titin zoo(gidan namun daji) dan tabbatar da komi yana daidai, kamin zuwan shugaban kasar.
An dai yita tsammanin zuwan shugaban kasar jihar Kano a kwanakin baya amma bai jeba, abinda har ya jawo cece-kuce, amma wannan karon akwai alamun masu karfi dake tabbatar da zuwan nashi.