Daruruwan ‘yan asalin jihar kano Dari uku da goma ne suka dawo daga kasa mai tsarki.
Da take karbar wadanda suka dawo a madadin gwamnatin jihar Kano, Darakta Janar na hukumar bunkasa saka jari Hama Ali Aware ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin tarayya da ma’aikatar harkokin kasashen waje kan kokarin da suka yi na ganin duk wadanda suka dawo sun an hada su da danginsu.
Misis Aware ta kuma ce “shirye-shirye sun yi nisa sosai inda gwamnatin jihar Kano za ta ba su horon koyon sana’o’i da nufin dogaro da kai.