Friday, May 29
Shadow

Jihar Katsina ta sallami mutum 51 da suka warke daga Coronavirus/COVID-19

Jihar Katsina ta bayyana cewa ta sallami mutane 51 da suka warke daga cutar Coronavirus bayan kulawar da aka basu.

Memba na kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar kuma babban Sakatare, Dr. Kabiru Mustapha ne ya bayyana haka ga manema labarai.

 

Yace jimullar mutane 13 ne cutar ta kashe a jihar wanda yace 5 daga ciki sun rasune a wajan killace masu cutar a jihar sai kuma sauran 8 da bayan sun rasune aka gano suna dauke da cutar.

 

Yace jihar tana jiran gwajin mutane 300 inda a yanzu ta samu mutane 285 masu dake da cutar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *