Gwamnatin jihar Naija ta bayyana tsige limamai 3 daga matsayinsu na limanci saboda jagorantar Sallar Idi wanda hakan ya sabawa dokar da gwamnatin jihar ta saka na hana Sallar Juma’i dan dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.
Daraktan harkokin Addini na jihar, Dr. Umar Farouq Abdullahi ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace an cire malam Abdullahi Ndakogi na garin Batagi saboda jagorantar Sallar Idi a garin.
Me magana da yawu Daraktan, Mustapha Tauheed ne ya bayyana haka inda yace an maye malam Abdullahi Ndakogi da wani limamin.
Shima dai wani Malam Muhammad Idris dake Rukunin gidajen Bosso an tsigeshi inda aka ce na’ibinsa ya karbi aikin limanci, an kama malam Idris ne da laifin jagorantar sallar Taraweeh data Tahajjud lokacin Azumin watan Ramadana.
Shima malam Auwal Yusuf daga Masafautar Kwantagora an dakatar dashi na tsawon shekara 1. Duk da ya bada hakuri inda yace baisan da dokar ba amma rashin sanin doka ba hujja bane kuma an bukaci ya nada hakuri a rubuce.