Saturday, July 20
Shadow

Jihohi 22 sun kashe Naira Biliyan 251 wajan Biyan Bashi a cikin watanni 9

Jihohi 22 a Najeriya sun kashe Naira Biliyan 251.79 wajan biyan bashin da gwamnatocin da suka gada suka bar musu cikin watanni 9 da suka yi suna mulki.

Hakanam kuma jihohin sun ciwo bashin Naira biliyan 310.99 a tsakanin wannan lokaci.

Sun ciwo wadannan basukanne duk da kudaden da suke samu daga gwamnatin tarayya wanda ake tura musu duk wata.

Hakan na kunshene a cikin bayanan yanda kowace jiha ta aiwatar da kasafin kudinta dake runbun tattara bayanai na Open Nigerian States.

Jihohin dai sune Abia, Akwa Ibom, Anambra, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Niger, Ondo, Osun, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba da Zamfara.

Karanta Wannan  Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Jihohin dai sun gaji jimullar bashin Naira Tiriliyan 2.1 dana dala Biliyan 1.9.

Jihohin dai sun gaji basukan albashi na watanni da yawa da ba’a biya ba da kuma basukan fansho na watanni da yawa da shima ba’a biya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *