fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Jihohin Arewa 4 da sukace ba zasu kori Almajirai ba

Maganar korar almajirai su koma jihohinsu na Asali da gwamnonin Arewa suka cimma matsaya akansa ya dauki hankula sosai inda wasu suka goyi baya, wasu kuma suna nuna rashin goyon bayan wannan batu.

 

Saidai duk da cimma matsayar da gwamnonin suka yi, wasu jihohin Arewar sun ki mutunta waccan yarjejeniya.

Hutudole ya kawo muku jihohi 4 da suka ce ba zasu kori Almajirai ba kamar haka:

 

Jihar Borno:

 

Jihar Borno kusan za’ace tana dsya daga cikin jihohin dake gaba-gaba wajan karbar Almajirai a Najeriya tun tale-tale zaka ji ana cewa akai wane gabas.

 

Gwamna Babagana Umara Zulum ya cimma matsaya cewa ba zai kori Almajirai zuwa jihohinsu na Asali ba, zai zamanantar da Lamarin karatun nasu.

Karanta wannan  Mutane tara sun mutu 12 sun jigata sakamakon hadarin mota akan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria

 

Jihar Yobe:

 

Jihar Yobe dake da makwautaka da Borno ta bayyana cewa ba zata kori Almajirai ba itama inda ta bi sahun Makwauciyarta.

 

Jihar Zamfara:

 

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa jihar Zamfara gidane ga almajirai dan haka ba zata koresu ba inda tace tana maraba da duk wadanda aka kora daga wasu jihohi.

 

Jihar Sokoto:

 

Itama dai jihar Sokoto, itace ta baya-bayannan data bayyana cewa ba zata kori Almajirai ba inda tace zata zamanantar da harkar Ilimin nasu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.