Gwamnonin jihohi 19 na Arewacin kasar nan suna shirin fara fitar da Alamajirai zuwa jihohinsu na asalin.
Babban sakaren kungiyar gwamnonin Arewa kuma sakataren gwamnatin jihar Filato, Danladi Atu ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a Jos ranar Lahadi.

Atu ya ce, “Ba mu kammala maida Almajirai daga yankin ba. Gwamnonin Arewa ba da jimawa ba zasu hadu su zabi ranar da zasu ci gaba da mayarda almajirai zuwa jihohinsu da suka fito. Amma hakan na iya kasancewa bayan hutun Sallah.
“A cewar Babban Jami’in Hukumar NGF, kusan Almajirai 11,000 ne da aka maida zuwa jihohinsu na asali yayin fara aikin farko wanda ya fara a watan Mayu.
Ya yi bayanin cewa an dakatar da tafiyar Almajirai na wani dan lokaci yayin bin umarnin kungiyar Shugaban kasa kan COVID-19 wanda ya sanya takunkumi a kan tafiye-tafiye a tsakanin jihohi.
Ya ce yanzu da aka janye dokar, jihohin Arewa za su sake ci gaba da aikin kwashe almajiran.