fbpx
Saturday, March 25
Shadow

Jirgi yakin sojojin Najeriya ya kashe kananan yara da yawa a jihar Naija

Yara dake tsakanin shekaru 5 zuwa 12 ne su 6 jirgin yakin sama na sojojin Najeriya ya kashe a Kuregbaa, karamar hukumar Shiroro dake jihar Naija.

 

Jirgin saman yakin sojojin Najeriya ya kai harinne kan gari bisa kuskure a yayin da yake kokarin kaiwa ‘yan Bindiga hari.

 

Mazauna garin sun bayyanawa Daily Trust cewa akwai kuma gidaje da yawa da suka lalace sanadiyyar harin wanda aka kai ranar Laraba.

 

Shugaban kungiyar hadaka ta karamar hukumar Shiroron, Salis Mohammed Sabo, ya bayyana cewa, an kai harinne da safe yayin da yaran ke dibar ruwa a wajan fanfan tuka-tuka.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *