fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Jirgin Kasa Ya Halaka Dabbobi 700 A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Wani abin alhini ya faru a yankin Masarautar Jere yayin da jirgin kasan da ke jigilar injiniyoyi masu aikin gyara layin dogo na Kaduna-Abuja ya halaka dabbobin da akalla yawansu bai gaza 700 ba.

Al’amarin wanda ya faru a daidai kasan gadar Azara, ya auku ne a yau Juma’a da misalin karfe 11:30 na safe.

Wasu tumaki da abin ya rutsa da su aka yanka
Majiyarmu daga Babban Ofishin ‘Yansanda (Area Command) na Jere ta tabbatar da cewa, daga cikin dabbobin da jirgin ya halaka akwai tumaki, awaki har da jakuna.

Majiyar ta kara da cewa, “Wannan Hatsarin jirgin kasan ya faru ne inda ya rutsa da tumaki, awaki, jakuna da misalin 11:30am yau (Juma’a) a gadar Azara da ke yankin Masarautar Jere a Karamar Hukumar Kagarko cikin Jihar Kaduna.”

Wasu tumaki da abin ya rutsa da su
Da aka tambayi majiyar ko me ya haddasa hatsarin, ta ce “sakamakon rashin hanyar tsallaka kogin Azara da ba a yi wa mutane da dabbobi ba don su rika samu suna tsallakawa musamman idan kogin ya kawo ruwa sai suka bi ta hanyar jirgin bisa tunanin cewa jirgin bai dawo aiki ba tun bayan harin da aka kai masa ranar 6 ga Mayun 2022.

Karanta wannan  Ba zan huta ba sai na samar muku da tsaro>>Shugaba Buhari ga 'yan Najeriya

Wurin da hatsarin ya auku

“Jirgin kasan yana daukar ma’aikata masu Maintenance (gyara) ne. Yau (Juma’a) ya taso daga Abuja zuwa Kaduna shi ne wannan tsautsayin ya faru. Dabbobi ne na wasu Fulani. Area Commander na ‘yansanda da kansa ya ziyarci wurin bisa rakiyar wasu jami’ansa don tantance abin da ya faru. Gaskiya abin babu dadi wallahi.” In ji majiyar tamu.

Tashar “Yanci Kaduna

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.