Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya fara aiki a safiyar Litinin bayan watanni 9 da kai hari kan jirgin.
An dauki sabbin matakai na tabbatar da tsaro a cikin jiragen, ciki har da tura ‘yan sanda dauke da makamai.

An kuma samar da wata na’ura inda fasinjoji za su iya haska tikitin jirgin da suka siya maimakon bin layi a nuna wa masu duba tikiti.