Fasinjan jirgin sama ya bayyana cewa jirgin daya hau daga Abuja zuwa Benin City ya kasa sauka a tashar jirgin saboda babu wutar lantarki.
Inda yace haka nan aka dawo dasu babban birnin tarayya Abuja saboda dare ne kuma ba wutar da zata haska titin zasu sauka.
Amma kanfanin jirgin saman ya basu hakuri akan wannan lamarin daya faru ranar 16 ga watan Yuni, inda yace za a kaisu washe gari.