Jirgin saman sojojin Najeriya ya babbaka mutanen kauyuka bisa kuskure a karamar hukumar Safana yayin da suka kaiwa ‘yan bindiga hari.
Rahoton ya kara da cewa wannan lamarin ya faru ne a daidai wurin da ‘yan bindigar suka kashe mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Aminu umar.
Wanda garin kokarin babbaka sansanin ‘yan bindigar suka babbaka jama’a wanda hakan yasa akayi asarar rayuka da dama.