fbpx
Monday, August 15
Shadow

Jiyanda sojoji da ‘yansandan Najariya suka tafka kazamin fada tsakaninsu hadda harbe-harbe da ya kai ga harbin fararen hula

Sojoji da ‘yansandan Najariya sun tafka fada tsakaninsu wanda ya kai ga aka harbi farar hula 2.

 

Lamarin ya farune a Yenagoa ta jihar Bayelsa. Sahara Reporters tace sojan ya je yana tuka mota sanye da kayan gida inda yayi aron hannu.

 

Dansandan dake bayar da hannu ya tareshi har ya bashi umarnin sakowa daga motar inda har ya kai ga ya mareshi.

Bayan da ya mareshine ya bayyana masa cewa shi soja ne, anan dai yayi ta bashi hakuri da cewa ya kamata maganar ta wuce.

Karanta wannan  Dakarun soji sun ceto wata dalibar Chibok da yaronta dan shekara hudu

 

Sojan ya tafi kamar ya manta amma daga baya ya sake dawowa da abokansa sojoji 2, anan ne fa suka afkawa ‘yansandan da duka wanda har ta kai ga dansanda daya ya kwace bindigar daya daga cikin sojojin, anan ne dayan sojan ya rika har bin kan mai uwa da wabi.

 

Sojojin dai sun tsere daga baya inda suka bar mutane 2 da suka harba cikin jini.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.