fbpx
Monday, June 27
Shadow

JNI ta maka Sarkin Zazzau a kotu bisa zargin karkatar da naira miliyan 20 diyyar fili

Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam, JNI reshen karamar hukumar Zaria ta maka Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli a kotu bisa zarginsa da karkatar da cekin kuɗi na naira miliyan 20 da ma’aikatar sufuri ta tarayya ta ba ta.

JNI ta ce an biya cekin cekin ne ga kungiyar a matsayin diyyar karɓe filinta na Kwalejin Larabci ta Jama’atu, ɓangaren maza, domin aikin hanyar jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Zariya a wani ɓangare na aikin titin jirgin ƙasa daga Ibadan zuwa Kano.

A karar da aka shigar a ranar 25 ga watan Afrilu, a babbar kotun jihar Kaduna, shugaban ƙungiyar da sakataren JNI reshen Zazzau, Zaharadeen Maccido da Usman Maccido, sun bukaci a saki cakin ɗin.

Karanta wannan  Bola Ahmad Tinubu ya shilla kasar Faransa don neman shawara

Masu shigar da ƙara sun yi ikirarin cewa sarkin ya rusa shuwagabancin JNI ne a matsayin wata hanya ta rufe musu baki.

Daily Nigerian.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.