Dr Dennis Otiotio, Shugaban Jam’iyar APC, reshen Jihar Bayelsa ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana da ƴancin shiga jam’iyyar amma har yanzu ba ɗan jam’iyar ba ne.
Otiotio ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, a wata tattaunawa ta wayar tarho a yau Talata.
Ya yi magana ne kan batun shigar Jonathan takarar shugaban kasa a 2023, yana mai cewa APC a Bayelsa ba ta da masaniyar cewar Jonathan ɗan jam’iyar ne .
“Tsohon shugaban kasa har yanzu bai zama dan jam’iyyar APC mai rijista ba. Yana da ‘yancin shiga duk jam’iyyar da ya ga dama.
“A shirye mu ke mu karbe shi a cikin mu, a matsayinmu na jam’iyyar siyasa mai muradin cin zabe, hanya daya tilo ita ce shigar da mutane cikin jam’iyyar,” in ji Otiotio.