fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Jonathan ya ki amincewa da tayin zama dan takarar shugaban kasa na APC a 2023 – Rahotanni

Rahotanni sun ce tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ki amincewa da tayin da wasu ‘yan fadar shugaban kasar suka yi masa na zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.

A cewar wani rahoto na musamman da SaharaReporters ta tattaro, an yiwa Jonathan tayin tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ne bisa sharadin cewa ya koma APC a hukumance tare da wasu gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party a shiyyar Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

Karanta wannan  Hallau rundunar sojin sama ta sake kashe shugaban 'yan ta'addan jihar Katsina tare da tawagarsa

Wasu daga cikin ‘yan fadar shugaban kasa da ake wa lakabi da “cabals” sun hada da wasu ‘yan uwa da abokan arziki na shugaban kasa Muhammadu Buhari, su ne ke bayan wannan kudirin.

Sai dai kuma an tattaro cewa tsohon shugaban ya ki amincewa da tayin kuma ya shaida wa cabal cewa ba ya da sha’awar tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.