fbpx
Friday, July 1
Shadow

Jurgen Klopp yana gab da rasa muhimman yan wasan shi guda biyu da Barcelona take hari

Liverpool bata siya yan wasa sosai ba a wannan kakar amma alamu na nuna cewa watakila ita ta rasa wasu daga cikin muhimman yan wasan ta bayan Barcelona ta kara dawowa kungiyar da neman yan wasa. Kuma rahotanni dagan kasar Sifaniya sun bayyana cewa sabon kocin Barca Ronald Koeman yana harin siyan Sadio Mane da kuma Gini Wijnaldum.

Luiz Suarez da Philippe Coutinho sun samu nasara bayan sun koma Barcelona daga Liverpool kuma duk da cewa yanzu Barcelona tana cikin rikici, babu dan wasan da zata nema yaki amincewa saboda ita babbar kungiyar a tarihin wasan kwallon kafa, yayin da itama Liverpool ta kasance daya daga cikin mayan kungiyoyin wasan kwallon kafa a duniya.
Gabadaya Sadio Mane da Gini Wijnaldum sun taba yin aiki tare da Ronald Koeman a baya, yayin da Mane yayi aiki da shi a kungiya shi kuma Wijnaldum yayi da shi a kasar Dutch. Kuma a halin yanzu idan har wani muhimmin dan wasan Liverpool ya bar kungiyar to zata ja baya kamar yadda tayi bayan tafiyar Luiz da Coutinho.
Jurgen Klopp yayi amfani da yuro miliyan 144 da Barcelona ta biya na siyan Coutinho wurin gina tawagar data lashe kofin Champions League,Premier League da kuma kofin duniya na kungiyoyi cikin shekara biyu, kuma har Klopp yana tunanin cewa ba sai ya karawa tawagar shi karfi ba a wannan kakar amma yanzu Barcelona tana so ya kawo mai matsala a yanzu idan har ta siye mai mayan wasan shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Za'a ba wanda ya lashe gasar tseren Marathon dala 80,000 a jihar Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published.