Sunday, June 7
Shadow

Juventus ma zata ragewa Ronaldo da sauran ‘yan wasanta Albashi

Munji Rahoton dake cewa Barcelona ta fada cikin matsalar tattalin Arziki saboda Coronavirus/COVID-19 kuma har ta yanke shawarar ragewa ‘yan wasanta Albashi.

 

To itama kungiyar kwallon kafa ta Juventus dake kasar Italiya inda Cristiano Ronaldo ke wasa ta bi sahu.

 

 

Kungiyar juventus ta sanar cewa zata rage kashi 30 bisa dari nadaga albashin yan wasan ta, kuma hakan zai sa Ronaldo ya rasa Euros miliyan 8.4. Sun yanke wannan shawarar ne saboda cutar Coronavirus/COVID-19 dake yin barazana ga rayukan al’umma tun shekarar data gabata.

 

Annobar cutar Covid-19 tasa gabadaya ayyukan Duniya basa tafiye yadda ya kamata kuma tasa an daga gabadaya wasanni nahiyar turai har sai abinda hali yayi.
An samu labari daga wurin Mundo Deportivo cewa shuwagabbannin juventus zasu rage albashin yan wasan su bada dadewa ba saboda basa buga wasa yanzu.
Ronaldo bai taba tunanin cewa rage albashin zai shafe shi haka ba, Amma a halin yanzu maganar rage albashi baza ta dame shi ba saboda ya bar kasar italia ya koma kasar shi ta Portugal a inda yake zaune tare da iyalin shi.
Ronaldo yace ba zai dawo kasar Italia ba har sai cutar coronavirus ta lapa. Kasar Italia tafi kowace kasar turai kamuwa da cutar Covid-19 kuma kimamin mutane 32,000 ne ke dauke da cutar kuma ta dauke rayukan mutane sama da 2000.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *