fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Juventus sun mayar da gabadaya hankulan su wajen siyan Haaland

An samu labari daga TuttuSport cewa Kungiyar Juventus sun shirya yin gasa da Real Madrid wajen siyan tauraron Dortmund Erling Braut Haaland,wanda ya kasance yana kokari sosai a wannan kakar wasan kuma yayi nasarar jefa kwallo a wasan da suka buga ranar sati da Schalke.

Juventus da Atletico Madrid suna harin siyan dan wasan gaba na kungiyar Napoli Arkadiusz Milik amma yanzu zasu fasa su mayar da hankalin su gabadaya wajen siyan Erling Haaland daga kungiyar Dortmund.
A shekara ta 2021, za’a sakawa Haaland farashin euros miliyan 75 cikin kwantirakin shi wanda hakan zai ba manyan kungiyoyin nahiyar turai damar siyan dan wasan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.