fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Ka baiwa Kowane dan Nageriya AK-47 ka gani idan zasu ji tsoron yan bindinga>>Fani Kayode ya caccaki Ministan Tsaro

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi bayan ya roki ‘yan Najeriya da su daina gudu idan yan bindinga suka kawo masu hari.

A kwanan ne Ministan Tsaro ya yi jawabi ga manema labarai kan mummunan hare-hare a wasu sassan kasar, Inda yayi kira ga mutanen Nageriya da su daina gudu idan yan bindinga suka kawo masu hari saboda wasu lokutan bindingogin ya ta’addan ba su da alburusai.

Dangane da wannan, Femi Fani Kayode yace;

Shin Ministan Tsaro yasan da cewa aikinsa shine kare rayukan mutane da dukiyoyin su amma ya gaza?

Ka baiwa Kowane dan Nageriya AK-47 ka gani idan zasu ji tsoron yan bindinga.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *