Gwamnatin Shugaba Buhari ta mayarwa Bishop din Sokoto martani, Matthew Kukah bayan daya cigaba da caccakar shugaban akan mulkinsa.
Inda a wa’azin daya yi ranar lahadi ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta gaza domin matsalar tsaro tayi yawa a kasar, ana daukar rayukan mutanen da basuji basu gani ba.
Amma mai magana da yawun Buhari ta kafafen sada zumunta, Garba Shehu ya mayarwa da faston martani, inda yace ya cire rigar malanta ta shiga siyasa yaga iya gudun ruwan shi.