Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta roki zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da cewa kada yawa bangaren ilimi irin rikon sakarcin da shugaba Buhari ya mai.
Malaman sun roki Tinubu da ya baiwa bangaren ilimi muhimmanci sosai.
Shugaban ASUU na FUT Mina, Prof Gbolahan Bolarin Ne ya bayyanawa jaridar Punchng da hakan, ya roki Tinubu kada yayi koyi da Buhari wajan bangaren Ilimi.
Yace bai kamata a bari dalibai su zauna a gida na tsawon watanni 8 ba kamar yanda gwamnatin Buhari ta yi.