fbpx
Monday, August 15
Shadow

Ka daina daukar kanka a matsayin wani shahararren dan siyasa, mataimakin Atiku ya fadawa Tinubu

Gwamnan jihar Delta kuma mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, wato Ifeanyi Okowa ya mayarwa da dan takarar APC raddi wato Tinubu kan tsokacin daya yi akansa.

Tinubu yace mataimakinsa Kashim Shettima yafi dan takarar PDP Atiku wanda hakan yasa Okowa ya mayar masa da raddi cewa babu wanda ya tambayesa wannan maganar.

Atiku cewa yayi ya nemi ya tsaya a matsayin abokin takararsa a shekarar 2007, saboda haka amsar wannan tambayar ya kamata ya bayar ba wai yace mataimakinsa yafi na Atiku ba.

Karanta wannan  APC batada dan takarar sabata a arewacin jihar Yobe da yammacin Akwa Ibom - INEC

Kuma a karshe Okowa yace Tinubu babban dan siyasa amma fa ya daina daukar kansa a matsayin wani shahararren dayafi sauran ‘yan siyasar kasar nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.