Kungiyar Yarabawan Najeriya ta Afenifere ta cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya daina yin Allah wadai akan matsalolin tsaro.
Inda tace kamata yayi shugaban kasar yayi kokari magance matsalolin da Najeriya ke fama dashi kan ya riga yin Allah wadai a koda yaushe.
Babban sakataren kungiyar, Chief Olusola Ebiseni ne ya bayyanawa manema labarai hakan a Akure birninin jihar Ondu.
Inda yace ASUU ta shiga wata shida a yajin aikin da suke amma Buhari Allah wadai yayi, kuma hakan yake cewa akan matsalolin maimakon yayi amfani da sauran watannin da suka rage masa ya magance matsalolin.