Jam’iyyar APC ta gargadi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso cewa ya gaggauta komawa APC tun kafin lokaci ya kure masa.
Mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar APC, Yakubu Mustapha Ajaka ne ya bayyanawa manema labarai hakan ranar lahadi.
Inda yace jihohi ba zasu sa tsohon gwmnan jihar Kanon ya kashe zaben shugaban kasa mai zuwa ba, saboda haka ya koma APC tun kafin lokaci ya kure masa.
Ajaka ya kara da cewa Kwankwaso na son zama shugaban kasa a jam’iyyar APC domin hadda shi aka kafa jam’iyyar kuma idan ya dawo zaiyi mulki a karkashinta.