fbpx
Thursday, May 26
Shadow

“Ka gaggauta janye dokar hana layuka miliyan 72 kiran waya cikin awanni 48”>>Kungiyar SERAP ta fadawa Buhari

Kungiyar dake kula da hakin bil’adama ta SERAP ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari daya janye dokar hana layuka kiram waya wa’yanda basu yi rigista da katin dan kasa ba.

A makon daya gabata ne gwamnatin tarayya ta bukaci kamfanoni dasu dakatar da kiran waya a duk wani layin da ba’yi mai rigista da katin kasa ba, wanda hakan yasa aka dakatar da layuka miliyan 72.

Yan kasuwa da dama suka bayyana cewa sunyi asarar miliyoyi, kuma yanzu abin ya kaiga kungiyar kare hakkin bil’adama ta bukaci Buhari ya gaggauta janye wannan dokar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.