fbpx
Monday, August 15
Shadow

Ka gaggauta korarar Fulanin daka nada a matsayin hafshoshin tsaron Najeriya, Kungiyar kare hakkin bil’adama ta fadawa shugaba Buhari

Kungiyar dake kare hakkin bil’adama a Najeriya ta HURIWA ta fadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya gaggauta korar hafsoshin Najeriya.

Kungiyar ta fada masa hakan ne ranar litinin a babban birnin tarayya Abuja, inda tace gabadayan Fulanin daya nada basa tsinanawa kasar da komai saboda haka ya maye gurbinsu da jajirtattun jami’ai.

Inda ta kara da cewa sun kasa magance matsalar tsaron da Arewa maso yamma ke fama dashi ta kashe mutane da kuma garkuwa dasu.

Sannan kuma ya kamata ya kama gabadaya jami’an da suka kasa dakatar da ‘yan ta’addan suka kai hari gidan kurkun Kuje dake babban birnin tarayya.

Karanta wannan  Rundunar sojin sama ta babbaka 'yan bindiga a mabuyarsu dake jihar Niger

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.