fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Ka hakura da takarar shugaban kasa in ba haka ba zaka ji kunya>>Kungiyar Ohanaeze Indigbo ta gayawa Atiku Abubakar

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta gayawa dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar cewa, ya hakura da maganar tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

 

Sakataren kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro ne ya bayyana haka inda yace ba zasu yadda da duk wata yaudara ta Atiku ba.

 

Yace tinda dai akwai Inyamurai a cikin masu takarar, to lallai su wakilansu zasu zaba amma ba zasu zabi Atiku ba.

 

Ya bayyana cewa ba zasu yadda da yaudarar Atiku kan maganar cewa wai wa’adin mulki daya zai yi ya baiwa Inyamuran ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.