fbpx
Monday, August 8
Shadow

Ka iya bakinka, Lokacin da Obasanjo yayi yaki dan hadin kan Najeriya kana can kana tatata, kuma ba dan shi ba da Buhari bai zama shugaban kasa ba>>Olusegun Bamgbose ga Garba Shehu

Shugaban jam’iyyar NNPP, Olusegun Bamgbose ya bayyana cewa ko kadan kalaman da kakakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  Malam Garba Shehu yayi akan Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo basu dace ba.

 

Ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar yau,Litinin inda yake inkarin cewar da fadar shugaban kasar ta yi Obasanjo shine shugaban masu raba kawunan ‘yan Najeriya.

 

Bamgbose yace a lokacin da Obasanjo yayi yakin basasa dan hadin Kan Najeriya, Garba Shehu na can titin Dutse a matsayin dan shekaru 5 yana tata.

 

Dan haka bai kamata ya gayawa Obasanjo wannan magana ba kuma Obasanjo ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ta hanyar yaga katinsa na PDP a lokacin zaben 2015.

 

Yace Obasanjon ya taka rawa sosai wajan nasarar da shugaba Buhari ya samu a zabe, badan shi ba da bai zama shugaban kasa ba, amma akwai taimakon Allah.

Karanta wannan  Dan uwan Buhari daya yi barazanar rusa APC ya fice daga jam'iyyar

 

Yace Obasanjo ya juyawa Goodluck Jonathan,  dan Kudu baya ya goyi bayan dan arewa, shugaban kasa,Muhammadu Buhari,  sannan a shekarar 1979, Obasanjo ya baiwa Shehu Shagari Mulki hakanan a shekarar 2007, Obasanjo ya mikawa Marigayi ‘yaradua Mulki dan haka bai kamata Fadar shugaban kasa da Arewa su manta da wannan abu da Obasanjo yayi ba.

 

Yace Obasanjo yayi tsufan da ba zai biyewa gwamnatin da bata aikin da ya kamata ba dan haka dolene ya fito ya fadi ra’ayinsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.