fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Ka kawar da kai daga doka ka sakar mana Nnamdi Kanu dan samun zaman lafiya, Inyamurai suka gayawa shugaba Buhari

Wata kungiyar Inyamurai ta nemi shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya sakar musu Nnamdi Kanu.

 

Kungiyar me suna ASETU tace su sun lamuncewa Nnamdi Kanu a sakar musu shi kuma duk sanda ake son ganinshi zasu gabatar dashi.

Sun yi kira ga shugaba Buhari da ya kawar da kai ga abinda doka tace ya biya musu bukatarsu saboda rike Kanun ya jefa yankinsu cikin matsalar tsaro.

 

Sun baiwa shugaba Buhari misalin ya da aka yi sulhu da ‘yan Naija Delta da Kuma Boko Haram Wanda kuma hakan ya kawo zaman lafiya.

Karanta wannan  Matsalar Tsaro: Ba sai kun sayi bindugu son kare kanku ba hukuma zata kare ku, gwamna Uzodimma ya fadawa 'yan jiharsa ta Imo

 

Sun ce dan haka shima Kanu suna kiran a masa irin wannan afuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.