fbpx
Sunday, May 22
Shadow

“Ka kyale Bishop Kukah ka shawo kan matsalar tsaron Najeriya”>>Dattawan Arewa suka fadawa shugaba Buhari

Kungiyar dattawan Arewa ta NEF ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari daya fuskanci yadda zai shawo kan matsalar tsaron kasar nan ya rabu da Bishop Kukah.

Mai magana da yawun kungiyar Dr Hakim Baba Ahmad ne ya bayyana hakan a Abuja, inda yace dama mutane irinsu Kukah ba kaunar Buhari suke ba, saboda haka ya share su ya fuskanci matsalar tsaron da kasa ke fama dashi.

Gwamnatin Buhari ta zargi Kukah cewa yana daya daga cikin dalilan dayasa kasar Amurka taki sayarwa Najeriya jiragen yaki, amma kungiyar dattawan Arewan tace bai kamata gwamnati ta riga mayar da martani sosai caccakarta da ake yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.