Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya gayawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cewa ya rufawa kansa Asiri da be baiwa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai mukami ba a gwamnatinsa.
Tinubu dai ya baiwa Tsohon gwamnan jihar Benue, George Akume mukamin sakataren gwamnatin tarayya, wanda shine aka rika rade-radin cewa za’a baiwa El-Rufai.
A martaninsa, duk da be kira suna ba, Sanata Sani yace da ka baiwa dan iya aiki da yayi azarbabi ya rika nuna yafi ka da mataimakinka iya aiki.