fbpx
Monday, January 18
Shadow

Ka rushe kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 babu abinda suke sai satar kudi>>PDP ga Buhari

Jam’iyyar PDP ta ce bata ga amfanin kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 ba na gqamnatin tarayya.

 

Tace babu abinda kwamitin yake in banda sanar da yawan mutanen da suka kamu da cutar da wanda suka mutu, sai kuma amfani da wannan yanayi da ake na cutar ana satar kudi.

Tace kamata yayi ace kwamitin ya shiga binciken ya da za’a gano rigakafin cutar kamar yanda sauran kasashen Duniya suke amma hakan ya faskara.

 

Sanarwar data fito daga me yada labaran PDP, Kola Ologbondiyan tace tana kira ga shugaba Buhari ya rusa wanna  kwamiti a bar NCDC ta yi yaki da cutar.

 

Tace kuma ta yi mamakin a cikin kasafin kudin 2021 babu tanadin siyo kayan yaki da cutar tace amma hakan ba abin mamaki bane dan dana gwamnatin ta Buhari babu abinda ta tabukawa ‘yan Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *