Jam’iyyar Adawa ta PDP ta yi kira ga mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da ya sauka daga mukaminsa saboda zargin da aka masa na cewa ya karbi Naira Biliyan 4 daga hannun mukaddashin shugaban hukumar hana rashawa, EFCC, Ibrahim Magu.
PDP tace Magune ya bayyana haka a binciken da ake masa.
Ta kuma yi kira da cewa shima shugaban hukumar zabe me zaman kanta, Mahmood Yakubu ya sauka daga mukaminshi saboda zargin yiwa APC magudi ta ci zaben gwamnan jihar Edo.
Sakataren yada labarai na PDP bangaren matasa, Emeka Kalu ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai, kamar yanda Independent ta ruwaito.