Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta roki shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tausayawa Nnamdi Kanu ya sakeshi.
Shugaban kungiyar, George Obiozor Ne ya bayyana haka inda yace shugaba Buhari ya saki Kanu da saura Inyamurai da gwamnatinsa ke rike dasu.
Ya bayar da shawarar cewa kamata yayi a yi sulhu da matasan yankin jihohin Inyamurai.
Ya kuma roki matasan yankin su dakatar da zaman gida dole da suke saka mutane inda yace hakan na shafar yankin nasu sosai.