fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Ka Tuba ka ajiye makamanka ko in Hallakaka>>Shugaban Chadi ga Shekau

Shugaban Chadi, Idriss Deby ya bukaci shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da ya mika kansa ko kuma ya kashe shi a mabuyarsa da ke Dikwa.

 

 

Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan da shugaba Deby ya jagoranci dakarunsa wajen kaddamar da farmaki kan mayakan Boko Haram tare da kashe mutun 100 daga cikinsu.

 

 

A yayin jawabi ga al’ummar Chadi ta kafar talabijin, shugaba Deby ya ce, Shekau na da damar mika wuya a yanzu, in ba haka kuma, a yi amfani da wuta wajen fatattako shi daga mabuyarsa.

 

 

Deby ya gargadi Shekau cewa, zai aika shi lahira muddin ya ki mika wuya kamar yadda aka bukace shi ya yi.

A makon jiya ne, dakarun Chadi suka kaddamar da farmaki kan mayakan Boko Haram, farmakin da aka yi wa lakabi da ‘fushin Boma’ bayan ‘yan ta’addan sun yi wa sojojin Chadi kwantar-bauna tare da kashe 92 daga cikinsu.

Karanta wannan  Gwamna El Rufa'i yayi fashin baki kan sauyawa jihar Kaduna suna

 

 

Shugaba Deby  ya lashi takobin cewa, ba zai taba amincewa da shan kashi ba a wannan gumurzu da mayakan Boko Haram da suka addadi kasashen Tafkin Chadi.

RFIhausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.