fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Ka yadda ka zama mataimakina>>Kwankwaso ya roki Peter Obi

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar jam’iyyar NNPP na shugaban kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, yana rokon Peter Obi wanda dan takarar shugaban kasa ne na jam’iyyar labour party da ya zama mataimakinsa.

 

Kwankwaso ya bayyana hakane a wajan bude ofishin jam’iyyar NNPP na jihar Gombe.

 

Sannan kuma yace idan Peter Obi ya zama mataimakinsa, hakan zai baiwa kabilar Inyamurai damar tabbatar da mafarkinsu na samun shugaban kasa a Najeriya nan gaba.

 

Yace auna tattaunawa dan hadewa da jam’iyyar Labour party amma abinda ya hana kaiwa gaci shine yanda Peter Obi din ya ki amincewa ya zama mataimakinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.