fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Kabilar Igbo mazauna jihar Kano sun nemi afuwa sakamakon rikicin da zanga-zangar SARS ta haifar A Jihar

Al’ummar Ibo da ke zaune a jihar Kano sun nemi afuwa ga gwamnatin jihar da kuma mazauna jihar kan rikice-rikice da asarar dukiyoyi da aka yi kwanan nan sakamakon zanga-zangar SARS.

Shugaban ‘yan kabilar Ibo a Kano, Igwe Boniface Igbokwe shine yiyi wannan kiran yayin da yake yi wa manema labarai karin bayani jim kadan bayan taron masu ruwa da tsaki da aka shirya kan tabbatar da tsaro a jihar.

Shugaban karamar hukumar Fagge, Alhaji Ibrahim Shehi shine ne ya shirya taron masu ruwa da tsaki a yankin karamar hukumar.

Rahotanni sun bayyana cewa, a kalla mutane 4 ne su ka rasa rayukan su yayin da motoci 15 su ka kone kurmus a sakamakon zanga-zangar adawa da rundunar SARS da a ka gudanar a jihar Kano.

Shugaban kabilar Igbo mazauna kano ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar da su yi abin da ya kamata a kan duk wanda ya gaza bin doka da oda.

Shima da yake jawabi, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Abu Sani ya bukaci shugabannin al’umma a Kano, musamman’ yan kabilar Ibo da su gargadi mutanan su kan su zauna lafiya a jihar.

Shima da yake jawabi, Shugaban Karamar Hukumar Fagge, Ibrahim Shehi ya ce taron masu ruwa da tsakin da a ka shirya ya tattauna matsalolin tsaro da kuma hanyar da za’a inganta shi.

A karshe ya yabawa gwamnan jihar Kano bisa kokarin da yake wajan tabbatar da tsaro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *