fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Kabusai Sun Shanye Gabadayan Tabar Sigari A Kasar Afrika Ta Kudu

Rahotanni daga kasar Afrika ta Kudu sun ce hamshakan kabusai sun karar da ilahirin kararen taba sigarin da suka samu kaiwa gare su, a shagunan dake sassan kasar.

Mabusa taba sigari a Afrika ta Kudun sun bazama zuwa shagunan sayar da sigari ne, bayan da gwamnati ta janye dokar haramta sayar da tabar da ta shafe watanni 5 tana aiki, domin dakile yaduwar annobar coronavirus ta hanyar hana cinkoson jama’a.

 

Tun a ranar Asabar da ta gabata, 15 ga watan Agustan da muke ciki shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya sanar da janye dokar hana sayar da tabar, da ma barasa a sassan kasar, matakin da ya soma aiki a ranar Litinin da ta gabata.
Bayanai sun ce fargabar cewa kila gaba gwamnati ta sake maido da dokar ya sanya dubban jama’a tururuwa zuwa shagunan sayar da taba sigarin suka kuma karar da duk wadda suka ci karo da ita.
Yanzu haka dai annobar COVId-19 ta fi yi wa Afrika ta Kudu illa fiye da kowace kasa a Afrika, inda take da adadin sama da mutane dubu 590 da suka kamu da cutar, yayinda annobar ta halaka wasu sama da dubu 11.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.