Wanda aka sace ‘yan uwansu a jirgin kasar dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja, sun caccaki ministan sufurin, Rotimi Amaechi kan kaddamar da yakin neman zabensa yayin da ‘yan Bindiga ke rike da ‘yan uwansu.
Sun bayyana cewa hakan bai dace ba, kakakin dangin wadanda aka sace din, Dr Abdulfatai Jimoh ne ya bayyana haka a ganawa da manema labarai.
Ya kuma gargadi hukumar kula da jiragen kasar kada a dawo da harkokin jigilar fasinja ba tare da an kubutar da danginsu dake hannun ‘yan Bindigar ba.
Ya bayyana cewa kamata ma yayi ace Amaechi murabus yayi bayan wannan harin. Yace kuma abinda ya kamata a mayar da hankali akai shine kubutar da danginsu sannan a dauki matakin da hakan ba zai sake faruwa ba kamin a dawo da harkokin sufurin.