fbpx
Monday, June 27
Shadow

Kada fa a sake a ce za’a dauki musulmi shugaban kasa kuma Musulmi Mataimakin shugaban kasa>>Kungiyar ta yi gargadi

Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Arewa, (NOSCEF) ta bayyana cewa, kada a sake a ce za’a dauki musulmi shugaban kasa kuma musulmi mataimakin shugaban kasa, ko kuma kirista shugaban kasa kuma mataimakinsa ma shugaban kasa.

 

Shugaban kungiyar, Ejoga Oyinehi Inalegwu ne ya bayyana haka inda yace yana taya Tinubu da Atiku murnar lashe zaben fidda gwani a jam’iyyunsu.

Yace amma su lura da banbancin addini dake tsakanin ‘yan Najeriya wajan fitar da mataimakansu.

 

Tuni dai hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta bukaci ‘yan takarar su mika wanda zasu musu takarar mataimakan shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.