fbpx
Friday, February 26
Shadow

Kada ku dauki doka a hannunku – Akeredolu da Fayemi sun yi gargadin yayin da rikicin Yarbawa da Hausawa ya kara kamari a jihohin Oyo da Ogun

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi sun bukaci ‘yan Najeriya da kar su dauki doka a hannunsu sakamakon tsananin tashin hankali tsakanin Hausawa da Yarabawa a wasu Jihohin Kudu Maso Yamma.

Rikici ya ta’azzara ne a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu, a jihar Ogun, lokacin da wasu ‘yan daba wadanda ake zargin makiyaya ne suka kai hari kan Orile-Igbooro da ke karamar hukumar Yewa North, inda suka kashe akalla mutane hudu.

An kone gidaje yayin da mutane da dama suka samu raunuka daban-daban a harin.

An kuma yi zargin cewa an kaiwa wasu al’ummomin yankin da yawa hari.

Wannan ya sa Olu na Ilaro da babban mai mulkin Yewaland, Oba Kehinde Olugbenle, suka yi kira ga gwamnati da ta kare rayuka da dukiyoyi a yankin nasa.

Matasa a yankin a karkashin inuwar Yewa North Patriotic Forum sun ba da wa’adin kwanaki bakwai ga makiyaya masu kashe mutane su bar yankin

Hakanan rikici ya barke a yankin Shasha na Ibadan, babban birnin jihar Oyo, da sauran su a Kudu maso Yamma.

Rikicin wanda ya barke a Ibadan ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mazauna garin, lalata dukiya da kuma raba mutane da muhallinsu.

Wannan ya sa gwamnatin jihar ta ba da umarnin rufe kasuwar ba tare da bata lokaci ba tare da sanya dokar hana fita a yankin.

Dangane da rikicin Hausa-Yarbawa, Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Yamma, da Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti sun roki bangarorin da ke rikici a yankin da kar su dauki doka a hannunsu.

Akeredolu ya yi kira ga mazauna, musamman Yarbawa da ke Ibadan, a Jihar Oyo, da kar su dauki doka a hannunsu sakamakon rikicin da ya barke a Shasha

A nasa bangaren, Fayemi ya yi kira ga bangarorin da ke fada da juna a yakin na Shasha, Ibadan da su lafa takobinsu.

Fayemi, a cikin wata sanarwa daga babban sakataren yada labaran sa, Yinka Oyebode, ya nuna juyayi ga gwamnati da mutanen jihar Oyo, musamman ma iyalai da suka rasa rayukansu da dukiyoyi yayin rikicin.

Ya kuma yaba wa Gwamna Seyi Makinde saboda daukar matakan gaggawa wajen kame barayin, gami da ayyana dokar hana fita.

Fayemi ya ce ba tare da la’akari da dalilin sabani da ya haifar da rikicin ba, sasanta rikicin cikin lumana ya kasance mafi kyawu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *