fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Kada ku rika cin zarafin Farar Hula>>kwamandan sojojin jihar Filato

Kwamandan rundunar tsaro ta musamman, Operation Lafiya Dole, Manjo janar Chukwuemeka Okonkwo, wanda ke wanzar da zaman lafiya a Filato da kewaye ya gargadi sojoji da su daina cin zarafin farar hula da ba su ji ba su gani ba amma su bi bayan masu laifi.

Okonkwo ya yi magana a wajen bikin bude wani aiki na musamman mai suna “Hakorin Damisa” a ranar Asabar a Bassa.
Aikin na Musamman, wanda zai dauki tsawon kwanaki hudu, da nufin rage rashin tsaro a wasu yankuna na kananan hukumomin Bassa da Riyom na Filato.
Kwamandan, wanda ya umarci sojojin da su kasance masu ƙwarewa wajen gudanar da ayyukansu, ya bukace su da su tabbatar da cewa kashe-kashen da ke a keɓe, hare-hare, fashi da makami, sace-sacen mutane, da sauran ayyukan ta’addanci sun ragu sosai.
“Kun zo nan ne domin ku mamaye, ku kawar da miyagun mutane kuma ku dakatar da duk wani nau’i na rashin tsaro a wannan yankin.
“Kada ku musgunawa fararen hula marasa laifi, su ba makiya bane. Irigwe, Fulani ko makiya ba masu laifi ba ne, don haka ku bi masu laifi kawai.
“Dole ne ku kasance kwararru a cikin halayenku kuma kuyi aiki yadda doka ta tanada.
“Ina son sakamako, ba uzuri ba. Don haka, ka tabbatar ka mamaye ka kuma dakatar da kashe-kashen, ”ya yi kira.
Dangane da dalilin gudanar da aiki na musamman, Okonkwo ya ce an yi shi ne don magance yawaitar kashe-kashe a sassan kananan hukumomin Bassa da Riyom.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *