A karshe dai an kammala zaben gwamnan jihar Ekiti yayin da yanzu ake kirga kuru’un da aka kada don sanar da wanda yayi nasara.
Kuma yanzu an kammala na kananun hukumomi goma na jihar yayin da dan takarar jam’iyyar APC Oyebanji ya kerewa abokan adawarsa da kuru’u dubu sitttin da biyar.
Inda shi hake da kuru’u 107,913 sai dan takarar SDP Segun Oni 43,122 yayin da dan takarar PDP Basi Kolawole keda 40,838.