Bam din da ‘yan kungiyar IPOB masu son kafa kasar Biafra suka danawa sojojin Najeriya ya tashi da mutane 2 daga cikinsu.
Kakakin sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka inda yace lamarin ya farune a jihar Imo.
Yace da kansu ‘yan IPOB din suka taka bam din bayan sun manta cewa sun sakashi ya tashi da sojojin Najeriya inda kuma ya tashi dasu.


Yayi kira ga Inyamurai masu son zaman lafiya da su rika sanar da hukumar sojojub ayyukan kungiyar na IPOB.