fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Kakaakin majalissar wakilai ya bukaci ‘yan Najeriya dake aiki a ofishin jakadancin Landan suba tsohon mataimakin shugaban sanata da matarsa da aka kama a kasar goyon baya

Kakaakin majalissar wakilai, Gbajabiamila ya bayyana cewa yayi mamaki sosai bayan da aka kama tsohon mataimakin shugaban sanatocin Najeriya da matarsa a kasar Landan.

A cikin wannan watan ne aka kama tsohon shugaban sanatocin Ekweremadu da matarsa Beatrice inda ake zarginsu da aikata lafin safarar sassan jikin dan adam.

Kakaakin majalisasar yayi kira ga ‘yan Najeriya dake aiki a ofishin jakadancin kasar Landan cewa su bashi goyon baya dari bisa dari domin a sako shi.

Kuma yace yana ganawa da babban kwamishinan Landan dan Najeriya domin a basu duk abinda ya cancanta wurin ceto shi, domin zargi ba shi ke tabbatar da laifi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.