fbpx
Friday, July 1
Shadow

Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal na shirin yin biyu babu, bai samu takarar shugaban kasa ba, kuma kujerar sanatan ma na neman gagararsa

Bayan shan kaye a zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na APC, kakakin majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal na kuma shirin rasa kujerarsa ta Sanata.

 

Wanda ya lashe kujerar tasa ta sanata, Bashir Machina yayi kememe yaki amincewa ya sauka ya barwa Sanata Ahmad Lawal.

 

Bola Tinubu ne dai ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar jam’iyyar APC wanda Sanata Ahmad Lawal na cikin wanda suka yi takarar.

 

Sanata Lawal dai na kokarin ganin APC ta saka baki an dawo masa da kujerarsa ta Sanata amma wakilin jam’iyyar na yankin Arewa maso gabas, ya gayawa Daily Nigerian cewa ba zasu yi katsalandan a harkar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.