Sanata Shehu Sani me wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar tarayya yayi wasu rubuce-rubuce da suka dauki hankulan mutane suka kuma jawo cece-kuce a dandalinshi na sada zumunta da muhawara da shafin Twitter.
Sanatan yayi maganane akan batun da wata kididdiga da akayi ta nuna cewa ‘yan sandan Najeriyane na daya a Duniya wajan rashin yin aiki yanda ya kamata, sanatan yace wasu zasu iya cewa a kori ‘yan sandanmu daga aiki tunda ance basu iya aikiba, ban yarda da irin wannan ra’ayiba.
Duka da dai sanatan be kama suna ba amma mutane da yawa sun fahimci cewa da gwamnan jihar Kaduna yake akan batun sallamar malamai da yace zaiyi bayan da aka musu jarabawar ‘yan aji hudu mafi yawanci su suka kasa cin jarabawar.
Masu sharhi da damane suka bayyana cewa be kamata sanata Shehhu Sani ya hada maganar ‘yan sanda da maganar korar malamai daga aiki ba domin abubuwane wanda suka sha banban kuma da yawa sunce korar malaman da Gwamna El-Rufai na Kaduna ke shirin yi hakan yayi dai-dai kuma sunyi Allah wadai da kalaman na sanatan.
Hka kuma a wani bayani daya rubuta da hausa shima wanda duk yake shagube ga gwamna El-Rufai na Kaduna akan korar malaman shima wasu sun mayar da amsoshi masu daukar hankali.