A cikin satin daya gabatane muka samu labarin cewa tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango ya tafi kasar Kamaru dan yin wasa acan, a wannan bidiyon Adamunne lokacin da ya karasa gurin da zai nishadantar da mutanen kasar ta Kamaru, irin yawan mutanen da suka taru don kallonshi, shi kanshi sun bashi mamaki.
A kiyasi, mutanen sukai kimanin mutum dubu goma, kuma a cikin bidiyon za’a iya jin wasu na kiran sunanshi.
Muna taya Adamu murna da fatan Allah ya dawo dashi gida lafiya.