fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Kalidou Koulibaly da Raheem Sterling sun bugawa Chelsea wasan Premier league na farko da kafar dama

Sabbin ‘yan wasa biyu da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta siyo, Kalidou Koulibaly da Raheem Sterling sun buga mata Wasan farko a gasar Premier league da kuma yin nasara.

 

Chelsea ta yi nasara akan Everton a wasan da Jorginho ya ci mata kwallon daya tilo, wannan yasa Chelsea ta samu nasara sau 20 kenan a wasannin ta na farko a gasar Premier league.

 

A tarihin kwallon kafa, babu kungiyar da ta samu irin wannan nasara da yawa haka a gasar Premier league a wasannin farko.

Karanta wannan  Tauraron dan wasan Najeriya, Mikel Obi yayi ritay daga wasan tamola

 

Shima kocin kungiyar, Tuchel ya bayyana cewa, sun yi kokari akan Everton saboda ‘yan bayansa duk sun haura shekaru 20.

 

Shima dai Koulibaly ya bayyana jin dadin nasarar da ya samu a wasansa na farko a gasar ta Premier league.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.